Kiev ta zargi ′yan aware da harba rokoki a kan wasu kauyuka | Labarai | DW | 23.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiev ta zargi 'yan aware da harba rokoki a kan wasu kauyuka

Su ma ana su bangaren 'yan awaren na zargin bangaren gwamnati da saba ka'idojin yarjejeniyar birnin Minsk.

Mahukuntan a birnin Kiev sun zargi 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha da bude wuta tare da harba makaman roka a kan kauyukan da ke yankin kudu maso gabashin kasar. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin biyu suka cimma a makon da ya gabata ke tangal-tangal. Yarjejeniyar dai ta bukaci bangarorin biyu da su janye manyan makamai da ma dakarunsu daga filin daga, batun da rundunar sojojin Ukraine din ta ce ba za ta janye manyan makaman ba, in har ana ci gaba da kai wa dakarunta hari. Rahotanni sun bayyana cewa yakin da bangarorin biyu suka kwashe tsawon lokaci suna yi ya fara shafar tattalin arzikin Ukraine, ta yadda darjar kudin kasar ke ci gaba da faduwa kasa warwas. Su ma dai ana su bangaren 'yan awaren na zargin bangaren gwamnati da saba ka'idojin yarjejeniyar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourrahmane Hassane