1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta iya maye gurbin Rasha kan makamashi

Usman Shehu Usman SB/MAB
April 19, 2022

Kasashen Turai na ci gaba da neman kawo karshen dogaro da makamashi daga kasar Rasha, sakamakon kutsen da kasar ta kaddamar na yaki a kan kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4A70a
Lituweniya | Makamashin gas na Rasha
Makamashin gas na RashaHoto: Vitnija Saldava/AP/picture alliance

Yayin da kasashen Tarayyar Turai ke cikin jimami kan yaki da ke faruwa a Ukraine, a yanzu suna neman ficewa daga dogaro da makamashi daga kasar Rasha, to amma kuma a gefe guda wata babbar barazanar tana girma. Wato batun makamashi ta iska mai kadawa, da motocin da ke amfani da lantarki da makamashin hasken rana hadi da wasu sinadaran hada na'ura mai kwakwalwa, duk suna matukar bukatar kayayyaki da sinadaren hada su. Amfani da na'urorin zamani wanda ke kara girma, abubuwa ne da ke matukar bukatar arzikin ma'adinai da sauran kayan hadawa, kuma a yanzu ana matukar karancinsu a yankunan duniya.

Babbar magana dai ita ce idan kasashen Tarayyar Turai suka juyawa Rasha baya to dole za su koma dogaro da China, domin a yanzu Rasha tana cikin masu fada a ji a batun iskar gas da Turai ke amfani da shi, yayin da ita kuwa China ta yi wa kowa fintinkau wajen na'urorin zamani da kayan hada su.

Sabiya: Bututun iskar gas na Rasha a matatar mai ta Pancevo
Sabiya: Bututun iskar gas na Rasha a matatar mai ta PancevoHoto: AP

Kayan hada na'urori da Tarayyar Turai ke amfani da su kashi 75 zuwa 100 cikin 100 duk suna dogara da wata kasa ne. Ma'adinai 30 mafi mahimmanci da EU ke bukata, 19 daga ciki duk sai a China suke sayowa. Raimund Bleischwitz kwararre ne a cibiyar kula da hada na'urorin rundunar sojan ruwa, wanda ya ce tuni China ta jima da shiryawa wannan yanayi.

Masana dai sun bayyana cewa dogaro da wasu kasashe a fannin ma'adinai zai dauki Tarayyar Turai shekaru da yawa kafin a shawo kansa, inda suka yi kiyasin har zuwa shekara ta 2030 ma'adinin Kolbat zai ci gaba da ninka kudinsa. Sannan a bangaren sufuri da na'urorin lantarki, zai kai nan da shekara ta 2050 domin ana matukar bukatar sinadaren hada batura da sauran abubuwa.