Kasuwar Volkswagen ta ja baya a Amirka | Labarai | DW | 03.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasuwar Volkswagen ta ja baya a Amirka

Rahotanni daga Amirka na cewar cinikin da kamfanin Volkswagen ko Bakswaja ya ja baya a Amirka tun bayan da aka bankado badakalar hayaki mai guba da motocin ke fidddawa.

Kamfanin ya shaida a wannan Talatar cewar yawan motocin da ya sayar a watan Oktoba da ya gabata ya ja baya matuka idan aka kwatanata da sauran kamfanonin sayar da motoci a Amirka din.

Wannan na faruwa ne daidai lokacin da hannayen jarin kamfanin na Bakswaja a nan nahiyar Turai ya fadi a kasuwannin shinku saboda halin da kamfanin ya shiga.

Masu aiko da rahotanni suka ce tun daga tsakar ranar yau aka hangi wannan matsala inda daga bisani hannun jarin kamfanin ya fadi da kashi 3 cikin 100.