Kasuwannin Kirsimeti masu burgewa a Jamus
Kasuwannin Kirsimeti sun kasance tun tsawon lokaci a Jamus. Ana kafa tantuna domin sayar da abubuwa masu ban sha'awa har ma da abinci har dubu biyu da 500 duk shekara. Ga wadanda suka fi birgewa.
Kasuwar Striezel ta birnin Dresden
Kasuwar Kirsimeti da ta fi dadewa a Jamus, ita ce Striezel da aka fara yin ta a shekara ta 1434. A ranar 23 ga watan Nuwambar da ya gabata, aka bude kasuwar karo na 588. ya kamata masu ziyara su dandana kayan kwalam da makulashe da ababen sha na Dresden da Striezel.
Kasuwar Christkindles ta birnin Nuremberg ta dawo
A al'adance, kasuwar Christkindles na budewa a ranar Jumma'ar farko ta karshen makon farko na fara shirye-shiryen bikin Kirsimeti da ake farawa a karshen watan Nuwamba na kowacce shekara. Birnin Nuremberg guda ne cikin manyan biranen Jamus da ke karbar bakuncin mutane miliyan biyu, kafin annobar corona. Bayan hutu na shekaru biyu, a bana an sake bude ta.
Kasuwar Kirsimeti ta Cologne da ta fin yin fice a Jamus
Daya daga cikin kasuwannin Kirsimetin Jamus da ake bayar da labari, ita ce ta Cologne da ke gudana a gaban babbar majami'ar birnin. Da mutane sama da miliyan hudu da ke ziyarta a duk shekara, wannan kasuwa na kan gaba cikin takawarorinta. Masu shirya kasuwannin, na jaddada bukatar dorewa.
Abin al'ajabin Kirsimeti a gaban ofishin gudanarwa na birnin Berlin
A wannan shekara, kasuwannin Kirsimeti kimanin 60 aka bude a Berlin. Kasuwar Kirsimeti da ke gaban ofishin gudanarwa na birnin, guri ne da ya kamata a ziyarta. Akwai tarin kayan wasa da suka hadar da wanda zai ba ka damar ganin baki dayan birnin da kuma wajen zamiyar kankara baya ga kayan kwalam da makulashe.
Kasuwar Kirsimeti ta birnin Leipzig na gudana cikin al'ada
Kasuwar Kirsimeti ta birnin Leipzig na gudana, a tsakiyar birni da ke da tsohon tarihi tun karni na 15. Hakan ya sanya ta zama guda daga cikin tsofaffin kasuwannin Kirsimeti a Jamus, kuma tana da rumfuna kimanin 300 abin da ya sa ta zama guda cikin wadanda aka fi ziyara. Kar ka sake a ba ka labarin kidan gargaji da ke tashi, a ofishin hukumar gudanarwar yankin kullum.
Kasuwar Kirsimeti ta Lübeck
Kasuwar Kirsimeti ta Lübeck na da al'ada ta sama da shekaru 400, kuma ana shirya ta a tsakiyar gine-ginen birni mai tsohon tarihi. Daya ne daga cikin biranen Hukumar Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO. Ana bude kasuwar a ranar 21 ga watan Nuwambar kowacce shekara. Akwai kayan kwalam da makulashe da na shaye-shaye, ana samun wasunsu a Jamus da Turai har bayan Kirsimeti.
Bishiyar Kirsimeti mafi girma ta Jamus a birnin Dortmund
Masu sha'awar kasuwar Kirsimeti, kullum suna murna da bishiyar Kirsimeti ta birnin Dortmund. Kasuwar Kirsimetin ta shekara-shekara, na bayyana bishiyar Kirsimetin mai tsawon mita 45 mai ganyyaki 1000 da aka yi wa kwalliya da fitulu da sauran kayan kawa 500. Akwai tarin rumfuna na sayar da kayan kwalam da makulashe da ma na ado da aka sarrafa da hannu.
Kalolin abincin duniya a birnin Essen
Wani abu ga kowa a kasuwar Kirsimeti ta birnin Essen da ke da rumfuna sama da 250 da mutane za su samu kayan kawa da zane-zane da aka sarrafa da hannu shi ne, abinci kala-kala daga sassan duniya baki daya. Kari kan hakan, a wannan shekara ta 2022 kasuwar ke cika shekaru 50 da kafuwa, abin da ya sanya ta zaama shekara mai muhimmanci.
Kirsimeti a kan ruwa a Lindau
Hoton kasuwar Kirsimeti ta "Harbor Christmas" a garin Lindau da ke Tafkin Constance na da rumfuna masu yawa da ya kamata a kai ziyara. Ana yin abubuwa masu kayatarwa. A ranar Asabar da ta biyo bayan ranar Saint Nicholas, shararrun masu linkaya a hunturu, na yin nutso a cikin tafkin da ruwansa ke da matukar sanyi.