Kasashen Larabawa na juya wa Iran baya | Labarai | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Larabawa na juya wa Iran baya

Tattaunawar a karshen mako na da nufin yin Allah wadarai kan abin da suka kira keta alfarmar Iran kan ofishin jakadancin Saudiyya a Teheran da Mashhad.

Kungiyar kasashen Larabawa za ta yi wani zama na gaggawa a ranar Lahadi bayan da kasar Saudiyya ta bukaci yin hakan dan tattaunawa kan rikicinsu da kasar Iran sakamakon farmaki da aka kaddamar kan ofishin jakadancin kasar a birnin Teheran.

Tattaunawar a karshen mako na da nufin yin Allah wadarai kan abin da suka kira keta alfarmar Iran kan ofishin jakadancin Saudiyya a Tehran da Mashhad a acewar Ahmed Ben Helli da ke zama mataimakin sakatare Janar na kungiyar a ranar Litinin din nan.

Bukatar wannan zama dai ta biyo rikicin da ake samu tsakanin kasashen biyu bayan kisan da mahukuntan na birnin Riyadh suka yi wa wani fitaccen malamin mabiya tafarkin na Shi'a Sheikh Nimr al-Nimr. An dai halaka malamin ne tare da wasu 'yan fafutika na Shia da wasu mayakan sakai da ke da alaka da Al-Qaeda bisa zargin ta'addanci.