Kasashen EU na tattaunawa kan Girka | Labarai | DW | 20.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen EU na tattaunawa kan Girka

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta isa birnin Paris a yau Juma'a inda za a tattauna da sauran kawayen kasashe daga kungiyar ta EU .

Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras ya fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters cyana da kyakkyawan yakini cewa gwamnatinsa za ta cimma muradin da ta ke da shi na ganin an tsawaita wa'adin da kasashen da ke binta bashi ya zuwa watanni shida nan gaba, adaidai lokacin da mahukuntan birnin Berlin na Jamus ke nuna adawa da wannan kari.

A cewar Firaminista Alexis Tsipras kasar ta Girka ta yi duk a binda ya dace wajen ganin an cimma wata matsaya da dukkanin kasashen da aka kulla yarjejeniyar bashin ta yadda zasu yi maraba da ita ta, hanyar mutunta dukkan bangarori da dokokin kasashen na Turai.

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta isa birnin Paris a yau Juma'a inda za a tattauna da sauran kawayen kasashe daga kungiyar ta EU da suka hadar da shugaba Francois Holland na Faransa inda za a tattauna kan batun yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta Girka.