Kasashe za su tallafa wa ′yan Rohingya | Labarai | DW | 23.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe za su tallafa wa 'yan Rohingya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashen duniya sun amince za su baiwa 'yan gudun hijiran Rohingya tallafin dala miliyan 340 don rage masu wahalhalun da suke ciki a kasar Bangaladash da suke fakewa a halin yanzu.

Kamar yadda MDD ta sanar, kasashen na duniya sun amince da hakan ne lokacin wani taron musamman da suka yi a birnin Geneva na kasar Switzerland. Taron dai ta hadin guiwa ce tsakanin kungiyar tarayyar Turai ta EU da MDD da kuma kasar Kuwet. Akwai ma wasu dala miliyan 50 din da kasashen suka amince za su samar da kayayyaki don musulmin marasa rinjaye na Myanmar.

Cikin watan Fabrairun badi ne dai za su amfana da tallafin. Kimanin 'yan Rohingyan dubu 900 ne suka tsere zuwa Bangaladash a karshen watan Agustan bana sakamakon rikici da sojin kasar Myanmar.