Siriya na son a sake fasalta dangantakarta da Rasha
October 15, 2025
Shugaban rikon kwaryar Siriya Ahmad al-Charaa ya shaida wa shugaba Putin cewa yana son a sake fasalta danganta a tsakanin Moscow da Damascus, a yayin ziyarar farko da ya kai Rasha a wannan Laraba tun bayan habarar da Bachar al-Assad da ke zama tsohon babban abokin dasawar fadar mulki ta Kremlin.
Shugaba rikon na Siriya ya ce suna mutumta dukkan yarjeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba a baya, amma kuma yana da kyau a sake fasalin yanayin dangantakar ta wata sabuwar hanya ta yadda Siriya za ta samu cikakken 'yancin kanta da hadin kai da daidaiton tsaro da zaman lafiya a yankunanta baki daya.
Daga nasa bangare shugaba Putin ya ce a tsawon gomman shekaru da suka gabata babban jogon dangatar kasashen biyu ya ta'allaka ne kan ci gaban al'ummar Siriya, sannan kuma ya ce alakar Moscow da Damascus alaka ce ta dogon lokaci mai cike da tarihi.
Jin kadan bayan ganawar shugabanni biyu da ta dauki sa'o'i biyu da rabi,karamin ministan harkokin wajen Rasha Alexander Novak ya shaida wa manema labarai cewa tawagogin biyu sun tattauna kan batun isar gas da kuma ayyukan makamashi da sufuri da yawon bude ido dgami da al'adu da kiwon lafiya.