1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kololuwan bikin Karnival

February 25, 2020

Mutum sama da miliyan daya ne suka halarci shagulgulan bikin raya al'adu na Karnival da a bana ya gudana a sassan kasar Jamus kamar yadda aka saba yi a duk shekara.

https://p.dw.com/p/3YOLy
Week That Was In Latin America Photo Gallery
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Espinosa

Yayin da aka kai kololuwar bukukuwan Karnival na wannan shekarar ta 2020 a wasu sassan kasar Jamus, birnin Kolon na kasar ya samu halartar baki da dama daga ciki da wajen kasar domin gudanar da bikin, inda jerin gwanon mutane da suka yi shiga dabam-dabam gwanin sha'awa suka karade titunan birnin cikin farin ciki da annashuwa.


Bikin da ke zama wata dadaddiyar al’ada a Jamus ana fara shi ne a ranar 11 ga watan 11 da kuma karfe 11 na kowace shekara. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kai kololuwar shagulgulan, inda mata ne suka chashe domin tunawa da ranar da suka karbi ‘yancinsu daga hannun maza a wancan lokacin, kawo yanzu haka lamarin yake, haka zalika ana gudanar da bukukuwan a nan birnin Bonn, Kolon dama wasu sassan kasar ta Jamus da ke daf da kogin Rhine. 


Ranar Litinin dai ita ce rana da ake gudanar da mafi girman taron na Karnival din, wadda kuma rana ce da ake sheke aya a manyan tituna birnin Kolon, inda babu babba ba yaro, su kuma shagunan sayar da barasa kakarsu ce ta yanke saka. Taron na birnin Kolon shi ne babban taro da aka kiyasta cewa kimanin mutane miliyan daya ne suka samu halartarsa, sai dai wani al'amari da ya nemi ya kawo tarnaki shi ne ruwan sama da aka tashi da shi a ranar bikin. Baya ga haka. Kafin kamalla bikin ne aka samu labarin kai wani hari a garin Volkmarsen da ke jihar Hesse, 'yan sanda ne suka bada sanarwar dakatar da bikin nan take bayan da wani direba ya kutsa cikin dandazon mutane da motarsa inda ya jikkata wasu da dama.