1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara kanana sun sha gurbataccen ruwa a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
May 24, 2024

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa kananan yara 70 sun kamu da cututtuka bayan sun sha gurbataccen ruwa sha a yankin Maradi.

https://p.dw.com/p/4gFWD
Hoto: picture-alliance/dpa

Gidan Talabijin din kasar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Dadin kowa da ke yankin Maradi, kazalika yanzu hakan yaran na kwance a gadon asibiti.

Hukumomi na zargin wata kungiyar mai zaman kanta da laifin gina rijiyar burtsatse a kauyen tare da ba wa jama'ar garin ruwan ba tare da binciken ingancinsa ba.

Ma'aikatar lafiyar Nijar ta ce jikin yaran na kaba kuma wani bangare na sassan jikinsu ya fuskanci nakasu, inda tuni aka yi wa wasu bakwai daga ciki tiyata 23 kuma na jiran yi masu aiki cikin gaggawa.

Shekarar 2001 yara kimanin dubu biyar sun samu tawaya a jikinsu sakamakon shan gurbataccen ruwa a garin Tsibiri na yankin Maradi da ke kudancin Nijar wanda ya jima yana tada jijiyoyin wuya tsakanin gwamnati da kungiyoyin kare hakin bil Adama.