1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kamfanonin sufurin Jamus sun sake ayyana shiga yajin aiki

Zainab Mohammed Abubakar
March 4, 2024

Matafiya a Jamus na shirin fadawa cikin wadi-na-tsaka mai wuya, sakamakon shirin shiga sabon yajin aikin kungiyoyin sufuri a wannan makon, mai nasaba da hauhawar farashin kayayyaki.

https://p.dw.com/p/4d8xW
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

 

Ma'aikatan filin jirgin na Lufthansa za su gudanar da yajin aikin kwanaki biyu daga ranar Alhamis, a cewar kungiyar ma'aikata, wadda ta zargi mahukuntan kamfanonin da nuna halin ko-in-kula- kan biya musu bukatunsu.

Kiran ya zo ne kasa da mako guda bayan yajin aikin da suka gudanar na karshe, a dai dai lokacin da su ma direbobin bas bas na fasinja da kananan jiragen cikin gari, ke shirin fara nasu yajin aikin kwanaki biyu daga gobe Talata, duk cikin yanayi na tsadar rayuwa da al'uumma ke fama da shi.