1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Kamala ta soki Trump kan yanke alaka da NATO

February 16, 2024

Batun dawowar Trump fadar White House na daga cikin batutuwan da shugabannin kasashen duniya suka tattauna a birnin Munich na tarayyar Jamus, musamman furucin da ya yi kan yanke huldar Amurka da NATO.

https://p.dw.com/p/4cVOr
Mataimakiyar Shugabar kasar Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar Shugabar kasar Amurka Kamala HarrisHoto: Johannes Simon/Getty Images

Mataimakiyar Shugabar Amurka Kamala Harris ta tabbatarwa da shugabannin kasashen duniya musamman kawayen Amurka cewa batun yiwuwar dawowar Trump fadar White House ba zai sauya manufofin kasar kan kawayenta ba.

Karin Bayani:Shin Trump zai dawo madafun iko?

A jawabin da ta gabatar a gaban shugabannin kasashen duniya da manyan jami'an diflomasiyya sama da 180, Kamala Harris ta ce dole ne Amurka ta ci gaba da kare muradun kawayenta, kasancewar hakan na daga cikin manufofin gwamnatin Amurkan.

Karin Bayani:Zaben Amirka: Shugabanin kasashen duniya na taya Joe Biden murna

Amurka ba za ta karaya ba ba kuma za ta janye ba daga goyon bayan da ta ke bawa kawayenta, acewar Harris, duk kuwa da furucin Trump na cewa zai yanke duk wata hulda da kungiyar tsaro ta NATO idan ya dawo fadar White House a matsayin shugaban kasa ba zai sa su karaya ba.