1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alakar Kamala Harris da Joe Biden

August 13, 2020

Kasa da kwanaki 100 a gudanar da zaben shugaban kasa a Amirka, matakin dan takara a karkashin jam'iyyar adawa ta Democrat Joe Biden na daukar Kamala Harris a matsayin mataimakiyarsa, ya janyo mabambantan martani. 

https://p.dw.com/p/3gvU8
USA Wahlen Kamala Harris
Kamala Harris da Joe Biden ya zaba a matsayin abokiyar takararsa Hoto: picture-alliance/AP Images/AP Photo/C. Kaster

Ana iya cewar babu abin da 'yar majalisar dattijai Kamala Harris ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasar ta Amirka Joe Biden da ya janyo mata wannan babban matsayi a siyasar kasar. Hasali ma kasa da shekara guda kenan, da ta soki abin da ya yi a shekarun 1970, kan tsarin rarraba yaran makaranta cikin motocin bus-bus, tsarin da  a cewarta ya kamata ya kawo karshen bambanci a rayuwar al'ummar Amirka: Akwai wata karamar yarinya a Califonia, tana bangaren 'yan aji na biyu a makarantar da ya kamata Amirkawa farare da bakar fata su halarta. Da Bus ake kai ta makaranta a ko wacce rana, kuma wannan yarinyar ni ce."

Harris ta yi wannan jawabin ne a lokacin muhawarar talabijin ta 'yan takarar shugabancin kasar ta Amirka a karkashin inuwar jam'iyyar Democrat gabanin zaben fidda gwani. Daga bisani Biden ya sha martani a kan wannan batun. A wannan lokacin 'yar majalisar na kokarin samun tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta Democrat ne, takarar da ta janye daga baya.

USA Kamala Harris  Primaries Debatte mit Biden
Muhawarar talabijin tsakanin Biden da HarrisHoto: picture-alliance/AP Photo/P. Sancya

Sai dai a 'yan makonni da suka gabata, Kamala Harris ta sanar da dalilan da ya sa har yanzu take dasawa da Biden a zauren hirar dare da gidan talabijin na Stev Colbert:  "Muhawara ce muka yi da ta kunshi ra'ayoyi mabambanta a kan wasu batutuwa. Ina bai wa Biden goyon bayana fiye da 100 bisa 100, kuma zan yi duk abin da ya dace domin na ga an zabi Joe Biden."

Alkawarin zai cika tun da ga dama?

Yanzu dama ta zo wa Kamala mai shekaru 55 a duniya domin ta cika wanannan alkawari nata, ganin cewar Joe Biden ya ayyana ta a matsayin mataimakiyarsa a fafutukar neman kujerar shugaban Amirkan. A cewar Amy Walter da ke sharhi kan al'amuran siyasa, da wannan mataki, Biden zai jefi tsuntsye biyu ne da dutse daya:
"Da farko dai ya kafa tarihi, na zabar bakar fata Ba'amirkiya kuma mace da ta hada asali da Indiya. Baya ga haka kuma 'yar majalisar dattijan tana da kwarewa, ta sha lashe zabuka kuma tana da masaniya sosai kan siyasar Washington."

US-Präsidentschaftskandidat Biden im Gespräch mit Arbeitern in einem Werk in Detroit
Kamala Harris yayin gangamin yakin neman zaben Joe Biden a MichiganHoto: Reuters/B. McDermid

An haifi Kamala Harris a Oakland da ke Kalifoniya a shekara ta 1964. Mahaifiyarta da ke zaman 'yar fafutuka kana mai bincike kan cutar cancer, ta kaura daga Indiya zuwa Amirka a shekara ta 1960. Mahaifinta farfesa ne a fannin tattalin arziki daga kasar Jamaika. Dukkansu sun kasance mambobin wata majami'ar Baptisma da kuma wurin bauta na 'yan Hindu da ke yankin da suke zaune.

Damawa da kowa, makamin yakar Trump

Wannan dai muhimmin batu ne ga zaben na Amirka. Wajibi ne 'yan Democrat din su tabbatar da janyo hankalin dukkan bangarori na al'umma, idan har suna muradin doke shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican. Kamara Harris dai 'yar siyasa ce da ba ta da tsoro, tana kokarin cimma muradun jam'iyyarta. A matsayinta na 'yar majalisar dattijai, ta kada kuri'ar tsige shugaba Trump wanda takan bayyana a matsayin mai nuna wariyar launin fata.