Kama masu zanga-zanga a Masar | Labarai | DW | 16.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kama masu zanga-zanga a Masar

Jami'ai a Masar, sun kama wadanda suka nuna turjiya da matakain mahukuntan kasar na amincewa bai wa Saudiyya wasu tsibiran kasar. Gwamman jama'a ne dai suka shiga ragar jami'n tsaro kan wannan batu a kasar.

'Yan sanda a kasar ta Masar sun kama mutane da dama daga cikin gungun 'yan adawa da suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga, bayan majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da mika wa Saudiyya wasu tsibirai guda biyu. Wani lauya mai zaman kansa ya bayyana cewar mutane fiye da 50 ne aka tsare daga ranar Laraba zuwa wannan rana ta Juma'a. 'Yan adawa dai sun zargi gwamnatin Masar da mika wa Saudiyya wadanan tsibirai domin samun tallafin kudi daga kasar.

A ranar Talatar da ta gabata ma dai wasu 'yan jarida sun fito kan titunan Alkahira babban birnin kasar don nuna rashin amincewa da yarjejeniyar kafin 'yan sanda sun tarwatsa su. Tun bayan da gwamnatin Al-Sissi ta Masar ta bayyana cewar ta cimma yarjejeniya da Saudiyya a kan tsibiran biyu cikin watan Afirilu ne, zanga-zanga ta ki ci ta ki cinyewa a wannan kasa.