Kalubalen kwallon mata a yankin Hausawa | BATUTUWA | DW | 07.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kalubalen kwallon mata a yankin Hausawa

A arewacin Najeriya mata masu son buga kwallon kafa na fuskantar kalubale daban-daban musamman daga iyaye da sauran al'ummar gari ganin yadda a yankin ake wa wasan kwallon kafa kallon sana’ar maza zalla.

 Albarkacin gasar kwallon kafa ta duniya da aka soma a kasar Faransa, ya sa mata da dama fitowa don bayyana sha'awarsu yayin da wasu da ke cikin sana'ar buga kwallon kafa a arewacin Najeriya suka yi tsokaci kan irin kalubale da kuma burinsu na kai wa kololuwa a wannan wasa na murza leda.

Mata 'yan wasan kwallon kafa na kungiyar Kaduna Queens Football Club sun yi fice a Najeriya, ana da akalla 'yan wasa 35 a karkashin kungiyar, kuma Grace KK matashiya mai shekaru 20 na cikin wadanda ke taka leda a kungiyar. A ganin ta kwallon kafa abu ne da kowace mace za ta iya yi. Duk da cewa Grace ta samu amincewar iyayenta, kasancewar a arewacin Najeriya, mata ba za su iya buga kwallo ba tare da sahalewar iyayensu ba, amma jama'ar gari sun so su sare ma ta gwiwa. Burin Grace dai shi ne ta kunyata masu sare mata gwiwa ta hanyar bunkasa a kwallon kafa har ma ta fita wajen Najeriya.

A dubi bidiyo 02:15

Mata na fuskantar kalubalen wasan kwallon kafa a Najeiriya

Ita kuwa Helen Ayuba wacce ke da irin wannnan buri, ta ce auren da ta ke shirin yi nan gaba kadan ka iya kawo mata cikas, sai dai sabanin wannan ra'ayi na Helen, a zahiri akwai mata irinsu Rose Emmanuel da duk da cewa ta yi aure kuma tana da ‘ya'ya uku amma ba ta daina taka leda ba. Ba kowace mace mai son buga kwallon kafa a arewacin Najeriya ce ta yi sa'a irinta Rose ba, domin akwai mata da dama da suke son bugawa amma kuma iyayensu da jama'an gari na nuna musu yatsa.

Yayin da mata daga sassan duniya daban-daban suka taru a kasar Faransa domin su buga kwallon kafa, fatan Grace da sauran abokan aikinta shi ne su ma wata rana a fafata da su a gasar kwallon kafa ta mata ta duniya. 

Sauti da bidiyo akan labarin