Kalubalen harkar sufurin jiragen sama a Najeriya | Siyasa | DW | 08.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen harkar sufurin jiragen sama a Najeriya

Najeriya ta ce za ta ci gaba da aikin kwaskwarima a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja, duk da matsin lambar da take samu musamman daga manyan kamfanonin jiragen sama na waje.

Wani ma'aikaci a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja

Wani ma'aikaci a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja

Tuni dai an yi nisa a kokari na sauyin fasali na Kadunar da ke zaman sabuwar mashigar birnin na Abuja har na tsawon wasu makwanni shida a nan gaba, to sai dai kuma gwamnatin Tarrayar Najeriyar na ci gaba da fuskantar turjiya musamman ma daga manyan kamfanonin sufurin jiragen sama na kasa da kasa da ke fadin basu da niyya ta karkatar da harkokinsu zuwa Kadunan. Kama daga Lufthansa na Jamus ya zuwa British Airways na kasar Birtaniya da ma South African Airline na kasar Africa ta Kudu dai, kusan daukacin manyan kamfanonin da ke daukar fasinjijoji su aje a Abujar, na cewa ba za su je Kadunan ba. To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce bata da niyyar saurara wa a cikin aikin gyaran da ke zaman mafi tasiri da kuma gwamnatin ke fatan zai sayin fasali a tashar ta Abuja.

Jirgin saman Lufthansa ya ce ba zai sauka a Kaduna ba

Jirgin saman Lufthansa ya ce ba zai sauka a Kaduna ba

Maimakon haka dai a fadar ministan sufurin sama na kasar Sanata Hadi Sirika gwamnatin kasar tana kalubalantar manyan kamfunan na jiragen zuwa ga ziyarar gani da idanunsu a filin saka da tashin jiragen saman na Kaduna da a fadarsa ke kama da na birnin Alkahirar Masar a halin yanzu. To sai dai kuma in har Abujar tai nasarar shawo kan adawa ta jiragen na sama, daga dukkan alamu jan aikin da ke gabanta a halin yanzu na zama na karuwa ta adawar daga kungiyoyi na fararren hula da 'yan uwansu na kwadago da suka share tsawon wannan mako suna ta nuna adawa ko dai a bisa manufofi na gwamnatin kasar kan mulki, ko kuma hali na rashi na lafiya ta shugaban kasar. Ko a Alhamis din nan mai zuwa ma dai, kungiyar kwadagon kasar ta NLC ta shirya wani gangami a biranen Legas da Abuja da nufin nuna rashin jin dadi da kari na talauci da rashin iya mulkin da suke zargin gwamnatin ta Abuja tai nisa a kai. Koda yake a fadar Sanata Sirika iskar da ke kadawa cikin kasar a halin yanzu tafi kama da siyasar neman mulki maimakon neman gyara. Abun jira a gani dai na zaman tasiri na siyasar ta 2017 a cikin harkokin kasar ta Najeriya dama kokari na kai wa ya zuwa karshen matsi na tattali na arzikin da ke zaman hujjar dagun hakarkarin a halin yanzu.

 

Sauti da bidiyo akan labarin