Kalubale ga rayuwar Mata da ′yan mata | Labarai | DW | 07.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kalubale ga rayuwar Mata da 'yan mata

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki al'ummomin kasa da kasa da abin da ta kira cin zarafin mata da yara mata.

Selmin Caliskan, sakatare janar ta kungiyar Amnesty International a Jamus

Selmin Caliskan, sakatare janar ta kungiyar Amnesty International a Jamus

Janar sakatare ta kungiyar a nan Jamus Selmin Caliskan ce ta bayyana hakan yayin hirar da ta yi da wata jarida da ke fitowa duk rana a Jamus, inda ta ce lamarin ya kazanta a shekarar da ta gabata duba da yadda aka samu karuwar tashe-tashen hankula nan da can. Ta kara da cewa abin damuwa ne yadda a ko yaushe ake samun karuwar mata da yara mata da ke shiga halin ni 'yasu yayin yaki. Caliskan ta ce ana cin zarafin mata yayin yaki ta hanyar yi musu fyade da muzguna musu inda ta ce ya zamo wajibi a yi maganin wannan matsala domin ganin an inganta rayuwar matan.