Kaddarori sun salwanta sakamakon ambaliya | Labarai | DW | 03.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kaddarori sun salwanta sakamakon ambaliya

Kasashen Jamus da Faransa na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama mai yawa da iska da wasu yankuna ke fusknata a halin yanzu.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela merkel ta nuna tausayawa ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in ambaliyar ruwa da ta wanke wasu garuruwa a yankin kudancin Jamus.

'Yan siyasa da ke jihar Bavaria da abun ya fi shafa sun yi alkawarin taimakawa wadanda bala'in ya ritsa da su a yankunan da ke jihar kamar yadda ministan kula da harkokin cikin gida na Bavaria Joachim Herrmann ya nunar...

" Idan ka duba dukkan yankuna da matsalar ambaliyar ta shafa, zaka ga cewar abun takaici ne, domin bamu taba tunanin hakan zai faru ba. Saboda ruwan sama mai yawa, sai gashi mun tsinci kanmu cikin ambaliya ta ko'ina, wanda kuma ya yi sanadiyyar salwantar abubuwa masu yawa har da rayka".

Tuni dai mutane suka fara daukar matakai na kasncewa cikin shirin ko ta kwana bayan ambaliyar da kawo yanzu ta yi sanadiyyar rayukan mutane 4, tare da katse wutar lantarki wa dubban mutane a jihar ta Bavaria da ke yankin kudancin Jamus