Jonathan ya gargadi majalisa game da neman tsige shi | Siyasa | DW | 04.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jonathan ya gargadi majalisa game da neman tsige shi

A Najeriya yunkurin tsige shugaban kasa da majalisar dokokin kasar ke yi na kara daukar sabon salo inda fadar shugaban Najeriya ta gargadi yan majalisar da su yi watsi da batun, tare da samun martani daga sassan kasar.

A Najeriya batun yunkurin tsige sugaban kasa da majalisar dokokin kasar ke yi na kara daukar sabon salo inda fadar shugaban Najeriya ta gargadi yan majalisar da su yi watsi da batun, abinda ya haifar da maida martani daga sassan kasar.

Wannan yunukuri na tsawatarwa ‘yan majalisar su yi watsi da batun tsige shugaban Najeriyar na zama kokarin murksuhe batun da sannu a hankali ake samun karin ‘yan majlisun dattawan, da ma majalisar wakilai da ke sanya hannu da jan daga a kan batun tsige shugaban na Najeriya a fito na fiton da ake ci gaba da fuskanta a tsakanin fadar shugaban Najeriyar da majalisar.

Domin kuwa wannan ne karon farko da aka ji ta bakin fadar shugaban Najeriyar a kan batun, inda a wata sanarwa, mai baiwa shugaban Najeriya shawara na musamman a kan hulda da jama'a Dr. Doyin Okupe ya bayar ya gargadi ‘yan majlisar a kan wannan batu. Wannan tuni ya sanya maida martani a kan illarsa ga dimukuradiyya. Mallam Buhari Muhammad Jega, darakta ne a cibiyar nazarin dimukuradiyya da ke Abuja:

‘'Wannan magana da fadar shugaban Najeriya ta yi wata mumunar magana ce ga tsarin dimukuradiyya, saboda in su majalisa da ke wakiltar al'umma suka ce shugaban kasa ya yi kaza to ai sai su bude kofar bincike a kan abubuwan da kuke cewa ya aikata, ya yiwu ma dai zargi ne. Saboda wadannan kalamai na nuna gwamnati ta dauki wani nauyi ne da bana dimukuradiyya ba, domin wannan ai kalamai ne na mulkin soja''.

Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan

Duk da kara zafi da wannan batu ke yi a Najeriyar, ‘yan majalisar na kallon lamarin a matsayin sandar duka da ke hannunsu, domin huce haushin da mamayar da 'yan sanda suka kai majalisar, tare da harba masu barkonon tsohuwa da suka yi a ranar 20 ga watan daya gabata, abinda ke kara sanya fuskantar fito na fito da ma jan layi a tsakanin sassan biyu.

Amma ga Barrsiter Mainasara Umar, masani a fanin harkokin shari'a na cewa kawai bukatar a fahimci yadda sassan ke aiki ba wai katsalandan bisa dalilai na siyasa ba.

‘'Ana yin abin ne a bai-bai saboda tsarin mulki ya yi bayani cewa bangare uku sune gwamnatin dimukuradiyya, akwai na zartaswa da majalisa da sashin shari'a. Amma maganar kace za ka koyawa wani bangare yadda zai aikinsa wannan ai azarbabiyya ne kawai. Domin ai bangaren zartaswa ma ba a kai ga gabatar da batun ba, balle a yi maganar wata kariya. Al'ada ce ta taso tunda farko su 'yan majalisar sun bada dama ana yi masu irin wadannan maganganu kuma ba abinda ke faruwa''.

To sai dai sanin cewa kasa da watanni shida ne ya ragewa wannan gwamnati ta kammala wa'adinta bayan kuwa aikin tsige shugaban Najeriya na cike da sarkakiya da ma matakai da ke bukatar lokaci ya sanya wasu 'yan jam'iyyar tofa albakacin bakinsu a kan batun Alhaji Isa Tafida Mafindi dan kwamitin zartaswa ne a jamiyyar ta PDP.

‘'Duk yadda aka yi shugaban kasa fa shine shugaban Najeriya ba wai dan jamiyyar PDP bane kawai ya wuce dan jamiyyar PDP, don haka akwai ‘yan Najeriya da ke da zuciya su kuma kai zuciya nesa amma wadanda suke da kwarmato a kasa za su dinga yi suna holo ba''.

Nigeria Parlamentspräsident Aminu Tambuwal

Kakakin majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal

Na dai yi kokarin jin ta bakin ofishin mai baiwa shugaban Najeriyar shawara a fanin hulda da jama'a day a fitar da sanarwar amma kuma hakan ya ci tura bisa cewa sanarwar da suka fitar ta wadatar.

Abin jira a ganin shine ko yunkurin tsige shugaban Najeriyar barazana ce da 'yan majalisar ke yi ko kuwa zasu iya ci gaba da aiawatar da ita idan sun dawo daga hutunsu a ranar 16 ga watan nan, a yanayi da zai zama tarihi ga dimukuradiyyar kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin