Jirgin yakin Turkiya ya harbo wani jirgin Rasha akan iyakar Syriya | Labarai | DW | 24.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin yakin Turkiya ya harbo wani jirgin Rasha akan iyakar Syriya

wasu jiragen yakin kasar Turkiya sun harbo jirgin yakin Rasha a kusa da kan iyakar kasar Syriya bayan gargadi da mahukuntan Turkiyan suka sha yiwa jiragen Rashan kan keta sararin samaniyar kasar.

Mahukuntan birnin Moscow sun ce ko kadan jirgin bai keta ta sararin samaniyar Turkiyan ba.

Wannan dai shine karon farko da wata mamba dake cikin kungiyar tsaro ta NATO ta harbo jirgin yakin Rasha tun bayan shekara ta 1950.

Mai magana da yawun fadar Kremlin yace al'amarin mai matukar tada hankali ne amma yayi wuri a yanke hukunci kan fadowar jirgin.

A ranar larabar nan ne dai ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov yake shirin isa Turkiya domin tattauna batun rikin kasar Syriya.