1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin sojin Jamus ya fadi a arewacin Mali

Mohammad Nasiru Awal ATB
July 26, 2017

A farkon wannan shekara Jamus ta kara yawan sojonjinta a Mali da mutum 350 da jiragen sama masu saukar ungula takwas ga rundunar ta MINUSMA.

https://p.dw.com/p/2hC1H
Mali Bundeswehr Tiger Kampfhelikopter
Hoto: Imago/M. Heine

Wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin Jamus da ke aikin wanzar da zaman lafiya karkashin rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Mali ya yi hatsari a arewacin kasar. Ahmad Makaila da ke kakakin rundunar da aka fi sani da MINUSMA shi ne ya sanar da faduwar jirgin wannan Laraba a yankin Gao, ya kara da cewa kawo yanzu ba a san makomar sojojin Jamus biyu matuka jirgin ba, haka zalika ba a san musabbabin faduwar jirgin ba.

A farkon wannan shekara Jamus ta kara yawan sojonjinta da mutum 350 da jiragen sama masu saukar ungula takwas ga rundunar ta MINUSMA. Yanzu haka kasar na da dakaru dubu daya da ke aiki a wani bangare na MINUSMA da kuma wata tawaga daban ta kungiyar Tarayyar Turai.

Hatsarin dai ya zo ne makonni kalilan da zaben 'yan majalisar dokokin Jamus da zai gudana cikin watan Satumba inda shugabar gwamnati Angela Merkel ke neman wa'adin mulki na hudu.