Jirgin ruwa ya kife a Lagos | Labarai | DW | 01.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin ruwa ya kife a Lagos

A birnin Lagos na tarrayar Najeriya mutane goma sun mutu kana wasu hudu sun yi batan dabo bayan da wani jirgin ruwa na fasinja ya kife da su.

Jirgin ruwan wanda ya tashi daga Badagry zuwa wasu kauyukan na bakin teku a Lagos, yana dauke da fasinja 19 sai dai  daga cikinsu biyar kawai aka ceto. Hukumar sufirin jiragen ruwa ta Lagos ta ce yawancin wadanda suke cikin jirgin ruwan ba su saka rigar nan ta ceto ba wadda doka ta tilasta sakawa don yin riga kafi. Yanzu haka dai 'yan sanda sun kame matukin jirgin ruwa tare da ci gaba da neman gawarwakin sauran mutanen.