Jawabin Merkel na sabuwar shekara | Labarai | DW | 31.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Merkel na sabuwar shekara

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel,tayi kira ga alummomin kasashen Turai dasu nuna karin hadin kai ,ayayinda Jamus ke shirin karban kujerar shugabancin kungiyar EU a gobe.A jawabinta na murnar sabuwar shekara,kamar yadda aka sabva,Merkel ta bayyana cewa,da hadin kann kasashen turan ne kadai,kungiyar zata iya kalubalantar matsalolin rayuwa,da tashe tashen hankula,da yakar taaddanci da yake yake.Shugabar gwamnatin Jamus din tace,idan ba a samu hadin kai ba,to babu shakka ba zaa iya cimma burin komai ba.A bangarwen harkokin cikin gida kuwa,Merkel tace Jamus na bukatar dada zage dantse a shekara ta 2007 ,idan tana muradin cigaba da bunkasa harkokin tatrtalin arzikinta,daya samarda guraban ayyuka sabbi kusan dubu 500,a shekarata 2006.Ta kara dacewa sauyi ya zama adole domin gyare gyaren mokomar jamus nan gaba,da cigaban nahiyar turai baki daya.