1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sharhin jaridun Jamus: Mali da Sudan sun dauki hankali

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
May 8, 2026

Jaridun Jamus na ci gaba da mayar da hankali, kan matsalar tsaro da ke ta'azzara a Mali da kuma yiwuwar barkewar rikici tsakanin Sudan da Habasha.

https://p.dw.com/p/5DVF3
Mali | Kidal | 'Yan Tawaye | MNLA
Masu kaifin kishin addni da 'yan tawayen Abzinawa na son kwace MaliHoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce: "Masu kaifin kishin addini da 'yan tawaye, suna matsa lamba ga gwamnatin sojan Mali." Jaridar ta ce sojojin gwamnatin Mali da mayakan sa-kai na Rasha sun fice daga sansaninsu, bayan da masu dauke da makamai da Abzinawa 'yan tawaye suka kwace wasu garuruwa na arewaci ciki har da Kidal. A lokacin da ta tabo musabbabin nasarar da 'yan ta'adda na JNIM da 'yan tawayen FLA suka samu, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce ba ya rasa nasaba da kawance da suka kafa da nufin ganin bayan gwamnati mai ci yanzu.

A nata bangaren FAZ.NET ta ce: "Rundunar sojojin haya ta Rasha, ta kasa katabus a rikicin Mali." Ta ce masu ikirarin kare Islama da 'yan tawaye na neman hanyar hambarar da gwamnatin mulkin sojan Mali, amma Moscow ba ta samar da taimako da ya dace ba ya zuwa yanzu. A nata bangaren ZEIT ONLINE  cikin sharhinta da aka wallafawa ta kafar Internet na cewa, Mali ta zargi wasu jami'an soja da hada kai da 'yan ta'adda wajen cutar da kasa bayan jerin hare-haren da suka haddasa kwace ikon sansanin soja a arewacin kasar.

Sudan | Yakin Basasa | Habasha | Rikici
Fargabar sabon yaki tsakanin Sudan da Habasha, ba ya ga yakin basasaHoto: Adrien Vautier/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Ita kuwa die tageszeitung ta yi sharhi mai taken: "Sudan da Habasha na gab da fadawa Yaki." Ta ce Sudan ta zargi Habasha da kai hari da jiragen sama marasa matuka a filin jirgin saman Khartoum, yayin da Habashan ta dora alhakin sabon rikici a yankin Tigray a kan Sudan. Jaridar ta ce, wannan take-taken yaki na kara hadarin karuwar yakin basasa da Sudan ke fama da shi yanzu haka. 

Duk da cewa gwamnatin Habasha ta yi watsi da zargin da ta danganta da maras tushe, amma Sudan ta kira jakadanta a Addis Ababa don tattaunawa bayan da ta zargi Habasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da zama kanwa uwar gami na harin birnin Khartoum. die tageszeitung ta ruwaito cewa, ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta mayar da martani mai zafi ta hanyar yin ikirarin cewa Sudan na taimakon 'yan tawayen TPLF da makamai da kudi da ma zama mabuyar sojojin da ke adawa da gwamnati.

Maroko | Rabat 2026 | Johann Wadephul | Nasser Bourita
Ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul da takwaransa na Maroko Nasser BouritaHoto: Rim Najmi/DW

A shafukan Welt Online batun da ya dauki hankali shi ne, yunkurin da Jamus ke yi na neman karfafa hadin gwiwa da Maroko ta hanyar dibar ma'aikata masu kwarewa daga kasar. Jaridar ta ce, a ziyarar da ya kai Rabat ministan harkokin waje na Jamus Johann Wadephul ya jaddada damarmakin tattalin arziki ga kamfanonin Jamus a wannan kasa ta Afirka. Ya nemi su rubanya daukar kwararrun ma'aikata, shi kuwa takwaransa na Maroko ya yi kira ga kanfanonin Jamus da su habaka saka hannun jari a kasar.

Welt Online ta kara da cewa, Jamus na son yin hadin gwiwa a bangaren kera motoci da bangaren makamashi da noma. Da ma dai bayan Afirka ta Kudu, Maroko da ke yankin Maghreb ta kasance abokiyar ciniki ta biyu mafi girma ga Jamus a Afirka kana muhimmiyar abokiyar tafiya a yankin da ke cike da rikice-rikice.

Afirka | Najeriya | Man Fetur | Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote Hoto: Noushad Thekkayil/NurPhoto/picture alliance

Batun zuba jari a nahiyar Afirka ya dauki hankalin Neue Zürcher Zeitung, inda ta yi sharhinta mai taken: "Yakin Iran, na kara wa mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka kuzari." Jaridar ta ce, attajirin nan Aliko Dangote da ya gina babbar matatar mai a kasarsa Najeriya na son rubanya masana'antu a nahiyar Afirka. Neue Zürcher Zeitung ta ce, mutane da yawa sun fara daukar yunkurinsa a matsayin almara lokacin da Dangote ya yi niyyar gina daya daga cikin matatar mai mafi girma a duniya a Najeriya. Dalili, kasar na cike da rudani da cin hanci. Amma yanzu ya zama abu na zahiri, matatar ta kai girman filayen kwallon kafa 4,000. Tana da ma'aikata 30,000, kuma tana iya sarrafa ganga 650,000 na danyen mai a kowace rana.

Jaridar ta kara da cewa yakin Iran da ya kai ga toshe Mashigar ruwan Hormuz yana tasiri a kan kasashen Afirka, soboda sun dogara da shigo da tataccen man fetur da taki daga waje. Amma Aliko Dangote ya yi alkawarin rage wa kasashen radadin karanci mai da suke fama da shi, inda  ya sanar da shirin gina babbar matatar mai ta biyu a Tanzaniya da ke gabashin Afirka a cikin shekaru hudu ko biyar masu zuwa. Neue Zürcher Zeitung ta ce, a yanzu babu wanda yake daukar sanarwar Dangote a matsayin mafarki.

Fassara: Mouhamadou Awal Balarabe

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani