1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Boren sojoji a Cote d'Ivoire da siyasar Ghana

Mohammad Nasiru Awal
January 13, 2017

Boren sojoji a kasar Cote d'Ivoire da rantsar da sabuwar gwamnati a kasar Ghana da rikicin jam'iyyar ANC a Afira ta Kudu sun dauki hankalin jaridun na Jamus.

https://p.dw.com/p/2Vl2c
Elfenbeinküste Meuternde Soldaten halten Verteidigungsminister fest
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Za mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka Cote d'Ivoire tana mai cewa:

Boren da sojoji suka yi a fadin kasa ya sa zababben shugaban kasa Alassane Ouattara daukar matakan kare kai daga tsoffin 'yan tawaye da ke cikin rundunar sojojinsa. Jaridar ta ce boren da sojojin suka yi na neman ba su alawus-alawus dinsu na sabuwar shekara, ya nuna fili yadda kasar ke cikin rashin sanin tabbas, kusan shekaru shida da kawo karshen yakin basasa. A ranaikun Jumma'a da Asabar na makon da ya gabata sojojin da suka tada kayar bayan sun karbi iko da garuruwa takwas. Ko da yake tattaunawar sulhu da aka gudanar a ranar Lahadi ta kwantar da hankali, amma bisa dukkan alamu kwanciyar hankalin ta wuci gadi ce.

Babban aiki a gaban sabon shugaban Ghana

Doguwar tafiya zuwa fadar shugaban kasa, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a labarin da ta buga game da rantsar da sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo a karshen makon da ya gabata.

Nana Akufo-Addo ya sha rantsuwar kama aiki a Ghana bayan ya lashe zaben watan Nuwamban 2016
Hoto: Reuters/L. Gnago

Jaridar ta ce a shekarun 2008 da 2012 Akufo-Addo ya fadi a zaben shugaban kasa, amma ya yi nasara a karo na uku, inda a ranar Asabar aka rantsar da sabon shugaban mai shekaru 72 da haihuwa. Sai dai tsohon lauyan rajin kare hakin dan Adam da kuma ya taka rawa a fagen siyasar kasar ta Ghana yana da jan aikin sake farfado da tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa da kuma kirkiro da guraben aikin yi ga matasan kasar da suka dora babban fata kanshi.

Rikicin cikin gida a jam'iyyar ANC

Gwagwarmayar neman rike madafun iko maimakon biki, wannan dai shi ne taken labarin da jaridar Neues Deutschland ta buga game da bikin cikar jam'iyyar ANC da ke jan ragamar mulki a Afirka ta Kudu shekaru 105 da kafuwa.

Shugaba Jacob Zuma a babban taron Jam'iyyar ANC a Soweto
Hoto: Reuters/J. Oatway

Jaridar ta ce Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi kira da hadin kan jam'iyyar ta African National Congress albarkacin cika shekaru 105 da kafuwarta. To sai dai a cewar jaridar ba a ganin hakan a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da a cikin watan Disamba za ta gudanar da sabon babban taronta inda za ta zabi sabon shugaba da jam'iyyar za ta so ya tsaya mata mata takara shugabanci kasa a zabukan 2019, kasancewa Shugaba Zuma ba zai iya sake tsayawa ba domin ya riga ya yi wa'adin mulki sau biyu. To amma yanzu haka an samu bangarori, kuma reshen mata na ANC ya zama na farko da ya goyi bayan da a tsayar da mace a matsayin wadda za ta gaji Shugaba Zuma, wato tsohuwar matarsa Nkosazana Dlamini-Zuma. Sai dai jiga-jigan jam'iyyar na zargin reshen matan da yin riga malam masallaci.