Japan ta yi gargadi ga Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 06.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Japan ta yi gargadi ga Koriya ta Arewa

Wannan gargadi dai na zuwa ne bayan da Koriya ta Kudun ta harba makamai masu linzami da suka ci nisan kilomita 1000 tare da fadawa kusa dakasar ta Japan

Japan Shinzo Abe PK nach den Wahlen

Firaministan Japan Shinzo Abe

Kasar Japan din dai ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tura cikakken sako zuwa Koriya ta Arewa tare da yin alawadai ga aikin harba makamai masu linzami har guda uku da kasar ta yi a ranar Litinin din da ta gabata. Jakadan kasar Japan a Majalisar Dinkin Duniyar Koro Bessho ne ya bayyana haka a wannan Talatar bayan wata tattaunawar sirri da Amirka ta kira domin mayar da martani bisa gwajin makaman na Koriya ta Arewa.

Shima da yake bayyana takacinsa dangane da gwajin makami masu linzamin da Koriya ta Arewan ta yi, jakadan kasar China a Majalisar Dinkin Duniya China Liu Jieyi cewa ya yi abin bakin ciki ne, ganin kasar ta Koriya ta Arewa ta aikata haka a lokacin da China ta karbi bakuncin shugabanni da suka halarci taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya na G20.