Jam′yyar PDP ta sami sabon shugaba | Siyasa | DW | 20.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam'yyar PDP ta sami sabon shugaba

Kwamitin zartaswa na jam'iyyar PDP a Najeriya Litinin ta zabi tsohon gwamnan Bauchi, Ahmed Adamu Muazu a matsayin sabon shugabanta da zai yi kokarin hade kan 'ya'yanta

A wani abun dake zaman kama hanyar bude sabon babi a cikin jami'iyar PDP mai fama da rigingimu, da yammaciyar yau jami'iyar ta tabbatar da zaben Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu a matsayin mutumin da take fatan jagorar ta zuwa nasara a zabukan shekara ta 2015.

Alhaji Ahmad Adamu Mu'azu dake zaman tsohon gwamna ga jihar Bauchi ne dai taron uwar jam'iyyar na kasa ya kai ga amincewa a wani taron da ya samu halartar masu ruwa da tsakin yayanta da kuma ake yiwa kallon wani yunkuri na kawo karshen tashe tashen hankulan da suka mamaye harkokin jamiyyar na lokaci mai tsawo.

Tuni dai murna ta kai har cikin cikin 'ya'yan gidan na Wadata dake kallon sabon zabin a matsayin wanda ke iya dinke tsakani, dama kila sake dora jami'iyyar bisa turbar tasirin dake fuskantar barazana ta asarar sa a yanzu.

Ibrahim Hassan Dan Kwambo dai na zaman gwamna ga jihar Gombe , kuma a cikin masu ruwa da tsaki na tabbatar da bullar Mu'azun da majiyoyi suka ce an kai ga ruwa rana kafin tabbatar da shugabancin nasa.

Karshen rikici ko kuma tabbatar da hutun jaki da kaya dai Mu'azun dan shekaru 59 a duniya dai na zaman dan takara na sulhu tsakanin masu hankoron sai ta sauyan da kuma masu tunanin dole ta zarce a cikin jami'iyar da ta share shekara da shekaru tana kisa tana shan romo amma kuma ke barazanar dandana daci na adawa a kasar. Wani rikicin cikin gidan jami'iyar a tsakanin Gwamna da shugabanta a baya Bamanga tukur a jihar Adamawa ne dai ya haukace ya tada hankalin kowa a gidan na wadata, to sai dai kuma a wannan karo kuma a fadar gwamnan jihar bauchi dake ci yanzu Isa Yuguda, tuni suka fara niyyar jifan shedan da nufin kaucewa duk wata fitinar iko a tsakanin gwamnan dake zaman jagoran jamiyyar a jihar da kuma Mu'azun dake zamanta babban mai gidan ta a koli.

Ko bayan shaidanun PDP dai sai kuma gwagwarmayar neman takara a jami'iyyar da ake yiwa kallon shedan babba da kuma daga dukkan alamu ke kwance ke jiran kamun ludayi na sabon shugaban a fadar Senata Ibrahim kazaure dake zaman mataimakin shugaban jami'iyar sashen arewa maso yamma , kuma jigo a cikin yan hautsina tsarin tabbatar da ikon na Jonathan kan kowa a cikin jami'iyar.

To sai dai koma ya zuwa wane lungu ne sabon shugabancin ke iya tabbatar da adalci kan kowa dai , a fadar sabon shugaban babu batun kamawa balle tunanin sai an karya a cikin mulkin da yace babu babu banbancin addini ko na kabila a cikinsa.

Ko bayan batun na adalci sai kuma fatan daukar kowa a cikin laimar da daga dukkan alamu ta sha suka da damina amma kuma ke da babban buri a tsakanin yayanta dake kallon har yanzu akwai sauran fata a fadar Inuwa

abun jira a gani dai na zaman kamun luddayi na shugabancin na Mu'azu dake da jan aiki na sulhunta tsakani tare da dinkin baraka da nufin tunkarar mummuna ta adawar APC.

Sauti da bidiyo akan labarin