Jamus:Badakalar injinan jabu na Volkswagen | Labarai | DW | 30.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus:Badakalar injinan jabu na Volkswagen

Gwamnatin Jamus na shirin gudanar da wani taro ranar Laraba mai zuwa domin tattauna batun badakalar injinan motocin diesel na jabu da aka bankado kamfanin Volkswagen ya aikata

Gwamnatin Jamus na shirin gudanar da wani taro na musamman domin tattauna batun badakalar injinan motocin diesel na jabu wanda aka bankado kamfanin Volkswagen ya yi a kan motoci sama da miliyan 11 da ya sayar a fadin duniya daga shekara ta 2009, lamarin da ya soma yin mummunar illa ga kasuwar motoci a duniya baki daya. 

Wannan taro wanda zai gudana a ranar Laraba mai zuwa zai hada wakillan gwamnati da na kamfanonin kera motoci na kasar ta Jamus da suka hada da Volkswagen da samfurin motocinta na Audi da Porsche da kuma kamfanin Daimler wanda ke kera motar Mercedes-Benz, da na kamfanin Opel da kamfanin Ford na Amirka gami da wakilan kungiyoyin kwadago. Taron zai nazarin makomar sana'ar kera motocin masu injin Diesel musamman a nahiyar Turai. 

A watan Satumbar 2015 ne dai hukumar kula da kare muhalli ta kasar Amirka ta bankado badakalar ta ha'incin da kamfanin na Volkswagen ya yi na saka wata na'urar da ke boye gaskiyar yawan gurbatacciyar iskar gas da injin diesel na motocin na ta ke fitarwa.Tuni dai kasashen Faransa da Birtaniya suka sanar da dakatar da saida motocin masu injinan Diesel da ma na man fetur daga shekara ta 2040.