Jamusawa na jimamin faduwar Germanwings | Labarai | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamusawa na jimamin faduwar Germanwings

Wannan ne karon farko a tarihin jirgin Germanwings da take samun hatsari irin wannan. Daga cikin wadanda suka rasu harda kananan yara 2

Bayanan da ke cigaba da fitowa dangane da jirgin saman Jamus na Germanwings, wanda ya fadi a tsaunukan kudancin Faransa, suna bada tabbacin cewa mutane 150 a ciki harda kananan yara guda biyu sun hallaka. A jawabin da ya bayar, kamfanin jirgin saman na Germanwings ya ce sai da jirgin ya gama kaiwa daidai bisan fara tafiyar tasa, sannan ya fara rikitowa daga sama, kuma ya shafe tsawon mintuna takwas yana rikitowa kafin ya fadi a cikin tsaunukan.

Firaministan Faransa Manuel Valls ya bayyana cewa a yanzu haka dai za a cigaba da binciken gano mafarin wannan hatsari ba tare da an fitar da duk wani dalili da ake hasashe ba.

Mahukuntan Spain sun ce suna kyautata zaton cewa wasu Jamusawa 'yan makaranta su 16 da suka je karin illimi a kasar na daga cikin fasinjojin wannan jirgi.

Wannan ne dai hatsarin farko kuma mafi muni a tarihin jirgin saman na Germanwings kuma mafi muni a Faransa tun shekarar 1974 sadda wani jirgin saman Turkiyya ya fadi a kasar mutane 346 suka riga mu gidan gaskiya. Ana sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ziyarci wurin da jirgin ya fadi a gobe laraba idan Allah ya kai mu.