Jamusawa na da ″mummunan″ tunani game da Musulmai | Labarai | DW | 15.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamusawa na da "mummunan" tunani game da Musulmai

Bincike: Kyamar addinin Musulunci da shirin tashin hankali kan wasu tsirarun al'umma na karuwa a Jamus.

Deutschland Mainz Plakat der AfD bei Pegida Demo

Zanga-zangar magoya bayan jam'iyyar AfD ta masu kyamar Musulmi a birnin Mainz

Wani binciken jin ra'ayin jama'a da jami'ar Leipzig da ke gabashin Jamus ta yi kuma aka wallafa sakamakonsa a wannan Laraba, ya gano cewa kimanin kashi 40 cikin 100 na Jamusawa na masu goyon bayan hana Musulmi yin kakagida a Jamus, yayin da kashi 50 cikin 100 suka ce a wasu lokutan Musulman na bari suna ji tamkar su baki ne a cikin kasarsu. A 2014 yawan bai kai haka ba. Binciken da ake yi bayan ko wadanne shekaru biyu an fara ne a 2002 don duba tunanin Jamusawa a siyasance. Mutane kimanin 2240 aka yi tambayoyin a wannan karo. Sakamakon binciken na zama shaida game da karuwar masu ra'ayin kyamar baki a Jamus, lamarin da ya yi muni sakamakon kwararowar 'yan gudun hijira musamman daga kasashen Musulmi irinsu su Siriya da Iraki da kuma Afghanistan. Binciken ya kuma gano karuwar kyamar wasu tsiraru inda kashi 10 cikin 100 suka ce Yahudawa na da angizo fiye da kima a Jamus.