1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta saki el Motassadeq gabanin lokaci

Zulaiha Abubakar MNA
August 9, 2018

Mounir el Motassadeq daya ne daga cikin wadanda aka samu da laifi a harin 11 ga watan Satumba 2001 a Amirka.

https://p.dw.com/p/32v9w
Jahresrückblick 2007 Januar Terror Mounir El Motassadeq
Hoto: CHRISTIAN CHARISIUS/AFP/Getty Images

Kasar Jamus za ta mayar da Mounir el Motassadeq dan asalin kasar Maroko wanda ke zaman shekaru 15 a wani gidan kurkuku da ke birnin Hamburg sakamkon samun sa da laifin harin 11 ga watan Satumban 2001 a Amirka, kasarsa ta haihuwa kamar yadda kakakin gidan yarin Frauke Koehler ta shaidawa manema labarai.

Mai shekaru 44 Mounir el Motassadeq zai fito daga gidan yari cikin watan Oktoba bayan kasar ta Jamus ta gargade shi da kar ya sake shigowa kasar.

An dai yanke masa hukunci ne tun shekara ta 2006 bayan binciken shari'a ya tabbatar da kasancewarsa daya daga cikin 'yan wata kungiyar ta'adda da kuma samun sa da hannu cikin aikata kisan kai.