Jamus za ta riƙa binciken iyakokinta da Austriya | Labarai | DW | 13.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta riƙa binciken iyakokinta da Austriya

Gwamnatin ƙasar ta ɗau wannan mataki domin rage yawan kwararra 'yan ci rani zuwa Jamus ɗin a daidai lokacin da wuraren karɓar 'yan ci rani ke yin ƙaranci.

Ministan cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere ya ce gwamnatinsu ta yanke shawarar soma ƙaddamar da bincike na wuccin gadi,na shige da fici a kan iyakokinta da Austriya inda daga nan ne dubban 'yan gudun hijirar ke kwararra musu.Ministan ya bayyana haka ne a birnin Berlin a taron manma labaran da ya kira.

De Maiziere ya ce ba za su amince da zaɓin da 'yan gudun hijirar suke yi, na nuna cewar dole sai ƙasar da suke so su samu mafuka za su je. A halin da ake ciki kamfanin sufirin jiragen ƙasa na Jamus Deutsche Bahn ya sanar da cewar ya dakatar da zirga-zirga tsakanisa da Austriya har zuwa gobe Litinin da misalin ƙarfe biyar na safe.Yanzu haka dai 'yan gudun hjijrar dubu 63 suka isa a birnin Munich na Jamus ɗin yayin da a jiya Asabar ka ɗai aka samu yan ci rani dubu 13. A cikin shekara an shirya Jamus za ta karɓi 'yan gudun hijirar dubu 800 amma kuma wuraran karɓar 'yan gudun hijirar na yin ƙaranci.