1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Bayer zai sallami ma'aikata

Gazali Abdou Tasawa
November 29, 2018

Shahararren kamfanin sarrafa magunguna na kasar Jamus wato Bayer, ya sanar da cewa zai sallami ma'aikata dubu 12 nan da zuwa shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/39AUA
Deutschland Aspirin Tabletten in der Bayer HealthCare AG
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Endig

Wannan na zuwa ne watanni kalilan bayan da ya sayi katafaren kamfanin sarrafa magugunan kwari da irin shuka wanda ake juya wa kwayoyin halitta na Monsanto. Kusan kaso 50 daga cikin 100 na ma'aikatan da matakin zai shafa dai sun hadar da na sashen kimiyyar sarrafa kayan noma su 4100 da na sashen sayar da magunguna su 1250 sai kuma wasu ma'aikatan dubu daya da dari daya na sashen sayar da magungunan da ba sa bukatar takardar izini daga likita. Kamfanin ya ce ya dauki wannan matakin ne domin sake tsarin tafiyar da ayyukansa da nufin inganta su. Kudi kimanin biliyan 54 na Euro ne dai kamfanin na Bayer ya zuba wajen sayen hannun jarin kamfanin sarrafa magungunan kwarin na Monsanto na kasar Amirka.