Jamus: Za a rantsar da sabuwar gwamnatin kawance
March 12, 2018Talla
Angela Merkel da Jagoran CSU, Horst Seehofer da kuma mukadashin shugaba SPD Olaf Scholz, sun rataba hannu a kan kudin yarjejeniyar mai shafi 177. Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel wacce ta ce a wannan mako za a rantsar da sabuwar gwamnati, ta ce tana fatan ganin gwamnatin ta samu nasara.