1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Yaki da ambaliya ta hanyar manhaja

Abdoulaye Mamane Amadou
July 26, 2021

Kwanaki bayan mummunan ambaliya hukumomin Jamus na shirin samar da wata manhajar da ka iya fargar da jama'a hadarin ambaliya, da duk lamura masu nasaba da sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/3y5lY
Bundespressekonferenz | Horst Seehofer stellt Fallzahlen politisch motivierter Kriminalität 2020 vor
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ministan cikin gidan kasar Jamus Horst Seehofe ne ya ambaci hakan, yana mai cewa bai ga dalilin rashin samar da manhajar ba  da akan iya amfani da ita ta wayoyin tarho, duk da yake a cewar sa da dama basu nuna gamsuwa kan wannan tsarin ba, a yayin da yake bayar da bahasi a gaban majalisar dokokin tarayya.

Ko baya ga tsarin fargar da jama'a ta wayar tarho, Jamus na shirin sake farfado da tsarin nan na kararrawa da kasar ta jima da su, to amma kuma aka yi fatali da su bisa rashin kulawa tsawon shekaru.

Hukumomi a jamus dai sun fuskanci matsin lamba daga al'ummar kasar bisa abin da suka kira sakaci na rashin daukar matakan da suka dace gabanin mumunan barnar da ambaliya ta yi wa kasar a tsakiyar wannan watan na Yuni.