Jamus tayi tir da hukuncin da Saudiyya ta yanke kan ′yan shi′a | Labarai | DW | 02.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tayi tir da hukuncin da Saudiyya ta yanke kan 'yan shi'a

Ma'aikatar harkokin wajen tarayyar Jamus tayi tir da Allah wadai akan hukuncin da mahukuntan Saudiyya suka dauka na hallaka wasu futattun mabiya a kidar Shi'a.

Wannan hukuncin dai na zama abin damuwa matuka a cewar ma'aikatar harkokin wajen Jamus a dai dai lokacin da ake samun matsalolin tsaro na ta'addanci.

Mafi yawancin mabiya tafarkin Shi'a dai 47 an yanke musu hukunci ne a ranar wannan Asabar wanda hakan ke zama hukunci mafi girma a shekaru 10 da suka gabata.

Daya daga cikin fttatttun mabiya Shi'a shi ne Nimr al-Nimr wanda hukumomin Saudiyya suka zarga da laifin kai hari ga 'yan sandan kasar.

Jamus dai ta kasance kasar baya-bayan nan da ta nuna damuwar ta kan wannan hukuncin da Saudiyya ta yanke kan mabiya akidar 'yan Shi'an a kasar.