Jamus ta yi nazari kan rikicin Katar a yankin Gulf | Siyasa | DW | 16.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ta yi nazari kan rikicin Katar a yankin Gulf

Toshe Katar da sauran kasashen Labarawa masu makwabtaka suka yi na ci gaba da daukar hankali, musamman saboda zuba jarin kasashen duniya a kasar, da kuma wanda kasar take zubawa a wasu kasashe.

Wolfenbüttel Bundesaußenminister Sigmar Gabriel trifft den katarischen Außenminister Scheich Mohammed Al Thani (Imago/photothek/T. Koehler)

Ministan harkokin wajen Jamus Sigma Gabriel da takwaransa na Katar Mohammed Al Thani

Jamus ta kasance daya daga cikin kasashen da ake samun zuba jari daga kasar ta Katar kuma yanzu haka Jamus na cikin masu neman kawo karshen wannan sabanin tsakanin Katar da sauran kasashen da Saudiyya ke jagoranci.

Wannan toshewar da kasashen na yankin Gulf suka yi wa kasar Katar ya shafi muradun Jamus. Rikicin ya zama kasada ga kamfanonin Jamus gami da harkokin tattalin arziki, tare da kalubale na siyasa. Tuni Sigma Gabriel da ke zama ministan harkokin wajen Jamus ya ce za a bi duk hanyoyin da suka dace domin magance matsalolin:

"Mun yi imanin cewa yanzu lokaci ne da ya dace a yi amfani da diplomasiya, dole mu yi magana da abokanmu Amirkawa, da na yankin, domin samun mafita. Musamman bude sararin samaniya da hanyoyin ruwa gami da magance matsalolin yankin."

Ana sa bangaren Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ministan harkokin wajen Katar ya tabbatar da cewa kasar ta shiga matsaloli sakamakon matakin kasashe makwabta.

Daya daga cikin abin da Jamus ke tsaro ka iya faruwa shi ne yaki tsakanin kasahsen na Larabawa, saboda babu wani mizanin iya tantance banbaci tsakanin bangarorin.

Sai dai a cewar Ulrike Freitag darakta a cibiyar kula da harkokin kasashen Gabas ta Tsakiya tilas Jamus ta ci gaba da bin matakan da ta saba domin samun nasarar da ake bukata musamman idan aka duba muradun Jamus a kasar Katar:

"A bangare guda ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta saba tattaunawa da kungiyoyin kasashen duniya da suka dace. Yayin da a daya bangaren Jamus ba ta fitar da kayayyaki sosai zuwa kasashen biyu, amma akwai hannun jarin 'yan Katar sosai a Jamus fiye da na Saudiyya."

Kuma ziyarar minsitan harkokin wajen katar, gami da na Shugaba Abdel Fattah Al Sisis na Masar tare da ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al Dschubeir cikin kwanakin da suka gabata suna kara tabbatar da rawar da Jamus za ta iya takawa wajen warware rikici a matakin kasashen duniya.

Wani abin da ke kara karfin wannan magana na zama rashin kudirin amincewa da Katar tana goyon bayan kungiyoyin ta'adda daga Majalisar Dinkin Duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin