Jamus ta soki wasu manufofin Amirka | Siyasa | DW | 05.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ta soki wasu manufofin Amirka

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya soki manufofin Amirka kan baututuwa da dama, kama daga harkar tsaro har ya zuwa ta diplomasiyya da tattalin arziki.

Deutschland Sigmar Gabriel Berlin Foreign Policy Forum der Körber-Stiftung (Imago/photothek/F. Gärtner)

Ministan harakokin wajen Jamus Sigmar Gabriel

 

A lokacin da Sigmar Gabriel ya yi jawabi a birnin Berlin kan manufofin harkokin wajen Jamus, ya ce matakan da shugaba Donald Trump na Amirka ke dauka na jawo wa kasar da Turai nakasu. 

Bisa la'akari da sauye-sauye da ake samu a manufofin Amirka karkashin jagorancin Donald Trump, Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya yi kira ga kasashen Turai da su fara daukan matakan kare kansu da kansu. Wannan dai ba ya rasa nasaba da barazanar da shugaban na Amirka ya yi na kin bayar da gudunmawar kudi da kayan yaki ga kungiyar tsaro ta NATO don ci gaba da kare kawayenta daga barazanar hare-hare, lamarin da Gabriel ya ce komabaya ne ga ita kanta Amirka da kasashen da abin ya shafa:

 "Donald Trump ya yi tsalle daga matsayinsa na jagoran tabbatar da tsarin cigaban kasashen yammacin duniya ya zuwa na canjin manufofin Amirka a kasashen duniya, lamarin da ke haifar da sakamakon maras kyau ga ci gaban Jamus da kasashenTurai. "

Ministan Harkokin Wajen na Jamus ya yi amfani da wannan dama wajen yin gargadi ga Kungiyar Tarayyar Turai da ta daina dogaro a kan Amirka wajen samun karbuwa a duniya. Dama dai shugaban na Amirka ya janye kasarsa daga yarjeniyoyi da dama ciki har da na tsugunar da 'yan gudun hijira da kuma ta sauyin yanayi. Maimakon haka ma dai Chaina na neman tsere wa Amirka a fannin kasuwanci, tare da tafiya kafada da kafada da kasashen Turai a nahiyar Afirka. Siegmar Gabriel ya ce lokaci ya yi da za a farfado da kyaukyawar danganta da ke tsakanin Turai da Amirka idan ba sa so a tsere musu:

"Amirka, kamar yadda na fahimta, ta yi watsi da matsayinta na fada ana ji a duniya baki daya. A takaice dai ta zama karen da ba ya cizo sai haushi. A tunaninmu Amirka na da rawar da za ta ci gaba da takawa a fannin tsaro duk da bambace-bambace da ke tsakaninmu. Babu shakka  muna son ci gaba da wannan hadin gwiwa kuma muna son ingantashi."

Sai dai kwararru na zargin wasu kasashen Turai da nuna son kai a wasu fannoni musamman ma na kasuwanci, lamarin da ya sa Birtaniya kada kuri'ar ficewa daga EU. Joseph Braml, jami'i a cibiyar nazarin dangantaka tsakanin Jamus da Amirka ya ce lokaci ya yi da Faransa da Jamus za su hada karfe wajen cike gibin da Amirka ta haifar a Turai a wadannan fannonin:


 " Ba za su kasance duk wadanda suka bi gurbin ba a nan. Amma tabbas za a samu jagorori biyu a Turai idan Faransa da Jamus suka cimma matsaya, musamman idan Jamus ta samu gwamnati da za ta iya aiwatar da manyan ayyuka, ba wai kawai gudanar da aikin jeka na yika ba. Ina tsammanin cewar za a iya daukar matakai masu yawa. Idan aka yi waiwaye adon tafiya, za a ga cewar matsaloli ne suka kawo cigaban Turai. Wata kila abin da zai faru kenan a wannan lokacin ma."

Shi dai masanin ya bi sahun Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel wajen nuna irin illar da ke tattare da matakin da ake sa ran shugaban Amirka zai dauka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila. Mista Gabriel ya ce wannan zai ruruta wutar rikicin yankin gabas ta Tsakiya, maimakon mayar da bangarorin da ke gaba da juna kan teburin tattaunawa da nufin samar da kasar Falasdinu da za ta yi zaman lafiya da makwabciyarta Isra'ila.