Jamus ta rufe mahakar ma'adanin kwal ta karshe
December 22, 2018Shugaban kasar Jamus Frank Walter Steinmeier ya jagoranci bikin rufe mahakar ma'adanin a yankin masana'antu na Rhur mai dadadden tarihi.
Gwamnatin tarayya da Jihohin North Rhine Westphalia da Saarland tare da kungiyoyin hakar ma'adanai ta IG BCE sun cimma yarjejeniya a shekarar 2007 domin kawo karshen hakar ma'adanin na kwal.
Fannin hakar kwal din dai ya samar da guraben ayyuka ga mahaka ma'adanai kimanin 33,000
Shugaban hukumar tarayyar Turai Jean Claude Juncker da Firimiyan jihar North Rhine Wesphalia na daga cikin wadanda suka halarci bikin.
A shekarar 1951 ne dai kasashe shida na tarayyar Turai da suka hada da Jamus da Italiya da Faransa Belgium da Netherlands da kuma Luxemburg suka sanya bangaren hakar ma'adanin kwal din karkashin hukuma guda ta ma'adanin kwal da karafa.