Jamus ta nemi bayani daga Amirka | Labarai | DW | 28.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta nemi bayani daga Amirka

Ana ci gaba da takaddama tsakanin Jamus da Amirka kan sauraron bayanai

Mahukuntan birnin Berlin na Jamus, sun nemi jami'an Amirka su yi bayani kan zargin satar sauraron wayar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Kasar Jamus ta bayyana cewa idan aka tabbatar da cewa hukumar leken asirin Amirka na satar sauraron maganar Merkel a cikin Jamus, za su gabatar da tuhuma ta miyagun laifuka. Shugaban Amirka Barack Obama ya ba da tabbacin cewa ba ya da masaniya kan sauraron bayanan da hukumar leken asirin kasarsa ke yi.

Ana zargin hukumar leken asirin ta Amirka da satar sauraron miliyoyi wayoyi a kasashen duniya, da suka hada da na wasu shugabanni.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh