1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nambiya ta samu tallafin corona daga Jamus

Abdul-raheem Hassan
July 8, 2021

Gwamnatin Namibiya ta samu tallafin corona da suka hada da takunkumi guda 500,000 da kuma gadajen asibiti 60,000 da safar hannu na likitoci guda 300,000.

https://p.dw.com/p/3wFHZ
Deutschland | Coronakrise: Krankenhaus in Aachen
Hoto: Ina Fassbender/AFP/Getty Images

Jirgin dakon kaya mallakin Jamus ya sauka Windhoek babban birinin kasar Namibiya, dauke da ton 70 na magungunan agaji, don taimkawa kasar Namibiya yaki da annobar corona.

Gwamnatin Berlin na shirin sake aike wa da karin kayan gwajin gaggawa da sauran kayayyakin agaji da suka kai dala miliyan 13, kasar Namibiya mai yawan mutane sama da miliyan biyu da rabi, na da mutanen da suka kamu da corona 97,100 wasu 1,662 sun mutu bayan kamuwa da cutar.