Jamus ta fiskanci kutsen na′urorin kwamfuta | Labarai | DW | 28.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta fiskanci kutsen na'urorin kwamfuta

A wannan rana ta Laraba mahukunta a kasar Jamus sun tabbatar da cewa suna gudanar da bincike kan kutse da aka yi wa tsarin na'urorin kwamfuta mallakar gwamnati sai dai kawo yanzu an shawo kan lamuran.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gidan Jamus ya ce ma'aikatun gwamnati da aka yi wa kutsen cikin na'urorinsu na kwamfuta sun binciki lamuran sun kuma kare bayanansu.

Ya dai kauce wa yin tsokaci na kafafan yada labarai na Jamus cewa kutsen Rasha ke da hannu a ciki, wacce ko a shekarar 2015 ta yi kutse irin wannan a majalisar dokokin kasar ta Jamus. Kafafan yada labaran dai sun ce masu kutsen sun so satar bayanai a ma'aikatun harkokin waje da tsaro a Jamus.