Jamus ta dau matakin rage gurbatacciyar iskar gas | Labarai | DW | 02.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta dau matakin rage gurbatacciyar iskar gas

Jamus za ta rufe wasu cibiyoyin samar da makamashi ta hanyar amfani da bakin gawayi da nufin rage fitar da gurbatacciyar iskar gas mai illa ga sararin samaniya.

Gwamnatin kasar Jamus ta dauki matakin rufe wasu tashoshin samar da makamashi ta hanyar amfani da bakin gawayi wannan kwa a wani mataki na neman rage fitar da gurbatacciyar iskan gas. Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a daren jiya Laraba bayan wata doguwar tattaunawa da ta gudana a tsakanin Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da abokanin kawancen jami'yyarta na SPD da kuma CSU.

Tashohin samar da makamashin da matakin zai shafa na samar wa kasar ta Jamus gigawatts biyu da rabi.Kuma hakan zai bai wa kasar ta Jamus damar cika burinta na rage nan zuwa shekara ta 2020 fitar da gurbatacciyar iskar gas da kashi 40 cikin dari akan wanda ta ke fitar wa a shekara ta 1990.