Jamus ta dakatar da visa ga jami′an Kambodiya | Labarai | DW | 22.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta dakatar da visa ga jami'an Kambodiya

Gwamnatin Jamus ta sanar da hana Visa ga Jami'an gwamnatin Kambodiya ciki har da Firaministan kasar Hun Sen sakamakon matsin lambar da kasar ta ke yi wa 'yan adawa.

Hun Sen (AP)

Wannan dai shine matakin da ke kan gaba cikin matakan da kasashen yammacin Turai suka dauka akan gwamnatin Hun Sen bayan da ya umarci kotun kolin kasar ta soke jam'iyyar (CNRP) wacce ke adawa da mulkinsa a fadin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun zargi Shugaban kasar da masu mara masa baya da amfani da kotunan wajen yin barazana tare da take hakkin 'yan adawa da kuma rufe kafafen yada labari masu zaman kansu.

Ya zuwa yanzu dai kakakin Jam'iyyar dake mulki a kasar Sok Eysan ya shaidawa manema labarai cewar gwamnatin ba ta da labarin wannan mataki da Jamus ta dauka.