1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Daimler zai janye motoci dubu 774 daga zirga-zirga

Abdourahamane Hassane
June 11, 2018

Ofishin ministan sufuri na Jamus ya ba da umarnin janye motocin dubu774 samfarin Marsandi na kamfanin Daimler masu aiki da man diesel daga zirga-zirga a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/2zJoJ
Deutschland Mercedes beim TÜV in Hildesheim
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Stratenschulte

Hukumomin na Jamus sun ce an yi ha'inci wajen kira motoci da aka yi da algushi wadanda ka iya sakin hayakin da ke gurbata muhali. A jamus kawai kamfanin zai janye motoci dubu 238, to sai dai shugabannin kamfani sun ce za su kawo gyara ga irin kura- kuran da aka samu da ka iya janyo matsalar gurbata muhali.