Jamus ta bukaci a taimaki ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 20.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bukaci a taimaki 'yan gudun hijira

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su kara yawan tallafinsu ga matsaloli da 'yan gudun hijira ke fiskanta a duniya, albarkacin ranar 'yan gudun hijira ta duniya.

A cewar Gabriel Jamus ba za ta iya biyan bukatar dukkanin 'yan gudun hijira da ke zuwa kasar ba, don haka akwai bukatar sa hannu na sauran kasashen na duniya a kokari na rarraba 'yan gudun hijirar da ma dakile tushen matsalar  da ke sa al'umma fita daga kasashensu.

Jamus dai ta sa himma a kokari na kare 'yan gudun hijira misali wadanda suka fito daga Siriya, abin da ya sanya mahukuntan na Berlin suka kara yawan kudade da suke kashewa cikin shekaru biyar har kawo yanzu.

A shekarar bara kasar ta kashe kudi Euro miliyan dubu da dari uku ta kuma karbi sama da 'yan gudun hijira miliyan daya a 'yan shrekarun nan wadanda ke gudun tashin hankali daga Afirka ko yankin Gabas ta Tsakiya.