1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Saurayi ya kashe tsohuwar budurwarsa

Abdul-raheem Hassan MNA
November 20, 2018

Mutumin mai shekaru 38 ya cakawa tsohuwar buduwarsa wuka da saurayinta da jaririnta mai tsawon makonni uku a duniya, sannan ya kashe kansa.

https://p.dw.com/p/38auo
Italien Francesco Amato, Mafiahäftling der Ndrangheta, nimmt Geiseln
Hoto: picture-alliance/Ropi

An fara binciken lamarin ne bayan da jami'an tsaro suka gano gawar mutane ukun a gabashin birnin Jena, sai dai ba a tabbatar da musababbin abin da ya sa shi aikata kisan ba, amma hukumomi na ci gaba da binciken lamarin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai loakcin da hukumomin Jamus ke shirin bayyana sabbin alkaluman kisa ta hanyar cin zarafi a fadin kasar baki daya, inda a shekara ta 2016 alkaluma sun nuna cewa mutane 147 ne aka kashe ta hanyar cin zarafi ko kisa da wuka.