1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na tallafa wa kasashen Afirka

Daniel Pelz SB
January 30, 2019

Tun karshen shekarar da ta gabata shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin zuwa jari na kimanin Euro milyan-dubu a nahiyar Afirka lokacin taro da kasashen nahiyar.

https://p.dw.com/p/3CSIF
Bundeskanzlerin Angela Merkel erhält amerikanischen Fulbright-Preis
Hoto: picture-alliance/M. Sohn

Lokacin zaman taron da ya gudana a karshen watan Oktoban da ya gabata na shekara ta 2018, shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bayyana cewar ko wanne lokaci ana la'akari na kasadar da ake fuskanta kan harkokin kasuwanci tare da gwada damar da ake iya samu.Sai dai duk da wannan yanayin shugabar gwamnatin Angela Merkel ta shaida wa fiye da kamfanonin Afirka 600 da suka halarci taron cewa Jamus tana shirye ta zuba jari a nahiyar. Tun watannin da suka gabata gabanin taro aka fitar da taswira kan irin kudaden da za a zuba jari. Masu kare muhalli gami da sauran 'yan gwagwarmaya suna neman ganin tsarin mai inganci, Uwe Kekeritz ke zama mai kula da mafufofun jam'iyyar kare muhalli a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag:"Kudaden zuba jari kan ci-gaba an fi yayatawa fiye da tsari, babu wani cikekken tunani da aka tsara game da haka, babu tsarin bin diddigi an bar shi a baya. Da wannan tsari kasashe marasa karfin tattalin arziki za su rasa wasu kudaden da suke amfana nan gaba. Akwai cikekken tsari kan muhalli da jin dadin rayuwa yanda za a aiwatar."

Compact with Africa - Teilnehmer beim Bundespräsidenten
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka