Jamus na son tsawaita ayyukan sojinta a Mali | Siyasa | DW | 23.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus na son tsawaita ayyukan sojinta a Mali

Muhawara ta kaure a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag game da yunkurin gwamnatin Angela Merkel na tsawaita wa'adin aikin sojojin kasar da ke a rundunar MINUSMA ta kasar Mali da watanni uku.

Von der Leyen in Jordanien Stützpunkt Luftwaffe Al-Asrak (picture-alliance/dpa/Bundeswehr)

Sojojin Jamus tare da Ministar Tsaron kasar Ursula Von der Leyen

Sojojin kasar Jamus sama da 500  tare da kayan aiki da suka hada da jirage masu saukar ungulu na yaki ne dai ke girke yanzu haka a kasar ta Mali a karkashin inuwar rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta MUNUSMA. Kuma a karshen watan farko na sabuwar shekara ce ya kamata wa'adin aikin na su ya kawo karshe.To amma kuma gwamnatin Angela Merkel na son tsawaita wa'adin aikin sojojin na Jamus a kasar ta Mali da watanni uku wato har ya zuwa 30 ga watan Aprilun 2018. To sai dai kuma wannan batu ya jawo babbar muhawara a tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar ta Jamus. Niels Annen dan majalisar dokoki ne daga jam'iyyar SPD:

Niels Annen SPD Bundestagsabgeordneter (picture alliance/Eventpress Hoensch)

Niels Annen dan majalisar dokokin Jamus daga jam'iyyar SPD

"Ya kamata a soma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta Mali, a kuma yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. Mali ta kuma saka kungiyoyin farar hula a cikin shirin. Idan an yi haka, mu kuma muna iya taimaka masu ta hanyar kungiyoyin kasar Jamus da ke aiki a kasar ta Mali. Kuma ba tun yau ba suka yi alkawarin samar da dokar tsarin zabe amma har yanzu shiru kake ji, kuma ya kamata gwamnatin Mali ta dage a fannin yaki da cin hanci a kasar."

To sai dai daga nata bangare jam'iyyar AFD ta masu kyamar baki a kasar ta Jamus ta bayyana takaicinta dangane da yadda ake tura sojojin Jamus suna salwantar da rayukansu a Afirka musamman a kasa kamar Mali da suka ce na kan hanyar zama tamkar Afganistan. Ita ma dai jam'iyyar 'yan gurguzu ta Die Linke ta bakin 'yar majalisar dokokinta Christine Buchholz zargin gwamnatin Angela Merkel din ta yi da fakewa da wannan siyasa ta tura sojojin kasar a Mali domin cimma wata manufa ta daban: 

Mali Feldgottesdienst im Camp Castor in Gao (picture-alliance/dpa/B. Pedersen)

Sojojin kasar Jamus a Mali karkashin MINUSMA

"Sam bai kamata sojojin Jamus na Bundeswehr su shiga wata rundunar tsaro ba, wacce ke aiki a kasar Mali tamkar wata rundunar mulkin mallaka"

A watan Disamba mai zuwa ne dai Majalisar dokokin Jamus din za ta kada kuri'a kan wannan batu. Sai dai tuni Ministan tsaron kasar Ursula von der Leyen ta sanar da cewa nan zuwa watan Yuni na 2018, Jamus za ta janye jiragenta masu saukar ungulu daga kasar ta Mali, inda ko a watan Yulin da ya gabata wani daga cikin jiragen ya fadi tare da kashe matukansa biyu.

Sauti da bidiyo akan labarin