Jamus na son a farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran | Labarai | DW | 20.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na son a farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran

A yayin ganawar manyan jami'an diflomasiyyar Jamus da Amirka a birnin Berlin a wannan Alhamis, Jamus, ta ce akwai bukatar a hanzarta ci gaba da tattaunawa tun kafin lokaci ya kure.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken sun yi ittifakin cewa har yanzu akwai yiwuwar ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran.

''Tattaunawar nukiliyar Iran din na cikin babban mataki. Muna bukatar ayi gaggawar ci gaba da ita, idan ba haka ba muradun takaita zirga-zirgar makamai da ake son cimma zai yi wuya a same shi.'' inji Baerbock

A watan Yunin shekarar da ta gabata aka fara farfado da yarjejeniyar dakile shirin makamashin nukiliyar Iran din ta 2015. Sai dai an dakatar da ita bayan da kasar Iran ta zabi  Ebrahim Ra'isi da ake siffantawa da mai ra'ayin rikau a matsayin shugaban kasa.